Uh Oh! You should not be able to read this. The reason is that this site uses complex stylesheets to display the information - your browser doesn't support these new standards. However, all is not lost, you can upgrade your browser absolutely free, so please UPGRADE to a standards-compliant browser. If you decide against doing so, then this and other similar sites will be lost to you. Remember...upgrading is free, and it enhances your view of the Web.

Welcome to http://www.Dandali.com: Fadi naka fadi nawa!
Menu

-o-o-

Dandali - Hausa Proverbs
View contributed Proverbs | Post your Proverbs | Proverbs with comments
 
Barka da zuwa Dandali.com - Karin Magana

Welcome to the Proverbs section of Dandali.com: This section contains list of Hausa Proverbs. If you know and would like to add your own Hausa Proverb, click here. To view your and other people's contributed Hausa Proverbs, click here. You may also view Hausa proverbs with comments and explanation given by visitors here.

Dandali - Karin Magana
[AN BAKARA GODIYA DA KWANAN GARKE.

Kowa ya rena mai labari in kaga mai gudu shi ne.

Gaskiya ta fi dokin karfe.

Abin mamaki kare da tallan tsire.

Ba neman aure ke da wuya ba, shiga ka fito.

In ka ji mutum yana tsoron dare ba a daure shi ya kwance ba.

Kowa ya ki tsotse hannu bai ji zakin miya ba.

Iska ba nauyi gare ki ba sai dai ka da itace.

Allah ya sauwake wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa.

Don mugun nufi ka dinkin lidifi.

In ka ga mutum na tsoron kira ya yi laifi.

Zakaran dawaki kukanka ba na alheri ba.

Sayen ragon malam, ya yi mai ya yi araha.

Daya matar yaro.

Wanda allah ya zuba wa garinsa nono bazai sha da tsamiya ba.

Mutanen duniya su kai mutum inda allah bai kai shi basu wahalshe shi.

Abin mamaki agwagwa da kin ruwa.

In ka rena dagumi ka ga kukumi.

Albasa ba ta halin kasa , da ba ta yi yaji ba.

Domin kifin badi ake koma.

Wanda ya ci ka, ya mallake ka duka da kai da iyalinka.

Ko wane gauta ja ne sai dai ba akai shi rana ba.

Kowa ka gani da tabarmarsa sai dai ya rasa wurin shinfidawa.

Maraya ba ya shkkar mutuwar uwar wani.

Bakon munafuki ba na mutum daya ba ne.

Inda yaro ya stinci wuri nan ya kan fi saurin tunawa.

An san biri yana da wuya akan daure shi agindi.

Birnin kura ba a sa kare dillanci.

Da nonon wuri da na dari duk farinsu daya.

Banza gudun harbabbe sai ya kai gawa nesa.

Gobara daga kogi, maganin nata allah.

Gyaran hanci ya fi gyaran gona.

Kome ka hakura da shi ka ga bayansa.

Mai kafa hudu ya kan fadi bare mai biyu.

In abu ya bace hankali bashi bacewa.

Abin wani dawuya, nemi naka

Makiyinka ba shi yabonka ko da ka kama damisa ka ba shi.

Makaho ba ya shakkar bata madubi.

Im baki ya zama daidai, hannu ba ya zama daidai.

Alhaki kare ne, mai shi ya kan bi.

Sandan girma ba a duka da shi, sai nuni.

Duhun damina maganin mai kwadayi.

Ba kyau ba a ke bida ga dakin gona, shi dai ya yi maganin ruwa.

Kisan damo hankali ne.

Mai kudundune a batta in ya sami shantu sai ya mike.

Ingarma gidan talaka haramun ne.

Kuwwa da kuwwa ba ta korar buzu.

Tsakuwa daya ba ta dabe.

Kowa ya yi maka kan kara, ka yi masa na itace.

Am fado daga kan dabino an zarce cikin rijiya.

Farin cikin barawo ya iske kofa tana bude.

Furar danko a shekara ana damu ba faraufarau.

Yawon dare ba na dan akuya ba ne.

Duba mini hanya, makaho ya so tsegumi

Ba a rena maje wuya sai yar wuka.

Annurin fuska kaurin hanji.

Bakar inuwa gwamma rana da ke.

Ba a yin nutso a masaki.

Tun ba a haifi uwar baduku ba borin turke ya ke yawo da jakar sa.

Wannan na daban ne malami da kudin kida.

Domin auki a ke yin kunu.

Bawan damina tajirin rani.

Saboda karen gidanka,ka kan ga karen gidan wani.

Kaka zan yi da abin da ya gagari wuta, inji kishiyar konanniya.

Haka tara in ji kishiyar, mai mageduwa.

Yaran zamani tun ba su tafasa ba su kan kone.

Gudu da waiwaya shi ya kawo mugun zato.

Komai na duniya wukar fawa ne, ya yanka guzuma ya yanka karsana.

Komai ya yi fari na da nagarta, amma ban da kurkunu,

Dole a zo, daki ya fada wa gurguwa da dan masu gida.

Har a nade kasa ungulu ba ta rama gayyar zabuwa.

Wanda za a kashe don an karairaya shi ba kome.

In kafafunka ba su iya taka kadarko sai ka ki ta kasa.

Masoyin gwado ba na kifi ba ne.

Kada dai a sha ruwa da ciyawa.

Mai bawa ba ya bauta.

Biri a hannun malami ya kan yi guda, ahannun bamaguje sai kuka.

Im muguwar kaza ta far shiga akurki, kowacce ta zo sai ta tsare ta.

Kowa ya keta riga tasa, ya san inda zare ya ke.

A bakin tsoho ne goro kan tsufa.

Mutum ba ya cewa kansa matsiyaci.

Tambarin talaka cikinsa.

In Allah ya so falke sai kayansa ya tsinke a gindin kaba.

Kowa ya kona rumbnsa, ya san inda toka ke kudi.

Sai wani ya rasa wani kan samu.

Tafasar tukunya ba ta rage gefe.

Abin da yaci doma ba ya barin Awai.

Tsigi ya ke barna, ana hushi da gauraka.

Kurum maganin mai tsegumi.

Shimfidar fuska, ta fi shimfidar tabarma.

Sai hali yayi dai dai a kan yi abuta.

In dai rakumi da girma kayansa ma da yawa.

In Allah ya ki addu'ar biri, sai ya mutu a gonar arna.

Farkon fada,nuna hannu.

Da babbar rowa gara karamar kyauta.

Koshin wake na ruwa ne.

In gani a kasa, an ce da kare ana biki a gidansu.

Bayan giwa sai barbje.

Mutanen duniya in ka sake sai su cimaka tuwo a ka.

Ganin gida kare ya kan zagi kura, amma ba a daji ba.

Wan da bai gode wa Allah ba, ya gade wa azabarsa.

In ka ji na kiya, samun dama ne.

Matsi shi kan sa kalangu zaki.

Maikwikwiyo shi ke da kare.

Samun sarari kuturu da gada a cikin rama.

Bera yana ganin rami, wuta ba ta kona shi.

Wukar fidar giwa ba girma gare ta ba , sai dai kaifi.

Cinikin duniya, diban nono.

A zuba shinkafa a ruwa a ga tashin shefe.

Wani kaya sai banufa, wace ayagi mai dan doro.

Mun koshi da nama, warinsa mu ke ji.

A so uwa a so danta don kowa da ranar sa.

Daga fake ruwa, sai shuka kabewa.

Im ba ka da wuri sai a sai da uwarka kana gani.

A kan mutu bare lala cewa.

Abu da yawa ya saba bacewa a fada ba takalmi ba.

Ana zaman karya, bamaguje ya zo gari ya iske ba masussuka.

Ka roka an ba ka da kunya balle an hana ka.

Ranar bikin farar kaza balbela ba gayya ce ba.

In anga macijiya a kwance sai a ce ba za tayi sara ba.

Kwanta ka mutu kaga mai kaunar ka.

Zama lafiya yafi zama sarki.

A rarrabe da magirbin sarar yakuwa da na rama

In kida ya sake rawa ma sai ta sake.

Karya akeyi tusa, ba ta hura wuta.

Mai ste gumi ba shi rabuwa da waiwaye.

An kai karar makauraci tun kaura ba ta zo ba.

In za a yi tukka a yi mata hanci don kada ta warware.

Muguwar miya ba ta karewa a tukunya.

Wutsiyar tsa ka mai gautsi.

Yaro bai san wuta ba sai ta kona shi.

Ba a raba harshe da hakori.

Mutum da gishirinsa, in ya ga dama ya dafa kaho.

Im ba za a zauna da gindi ba, ba a kuwa zauna da ka ba.

In za ka huta,ka huta a babar inuwa.

In kana cin baure, bari tona cikinsa.

Fade-fade ba yi ba ne, an ce za ayi tsarkiya da kunkuru.

Kowa ya rena tsaiwar wata ya hau ya gyara.

Kifi ba shi kiba sai da naman yan'uwa.

Ba a cewa maci wake sha ruwa.

Mai da ruwa rijiya, ba barna bane.

Kowa ya aikata abin da ya ke so, zai ga bakin ciki.

Mun gaji da kyau, hali mu ke nema.

Kana da aiki, zuwa kano da kayan gamba.

Ko cikin tumaki, rago ka zuwa fada.

Kowa ya ci ladan sarki,ya yi masa yaki.

Ba a kwace wa kuturu zobensa.

In ka ji saki-saki ba a kamu ba.

Ko ina ka ga hanya gida zata.

Makiyin ka ba ya ganin ramar ka.

Mutum fari ne, shi ke rina kansa ya zama baki.

Allah ya kara wa kogi ruwa, Kududdufi ya samu.

Na shiga ban dauka ba, bata fid da barawo.

Domin rana daya ba a kin guzuri.

Im babu kira mai ya ci gawayi.

Abin da ruwan zafi ya dafa, in an hakura ruwan sanyi ma zai dafa.

In da rabon kura a takobi, sai a sayar da shi a sayo ma ta akuya.

Raina girman kuka ,gabaruwa ta fi ta.

Karfin kiri na mai ne.

Wasan kokawa ba na gurguwa ba ne.

Wani tsuntsun na gudun ruwa agwagwa a ciki ta ke kwana.

Samun yarda da dodo ke sa a shiga ruwa lafiya.

Ranar tsafi bunsuru ke kudi.

Shirin zaune ya fi na tsaye.

Hanyar lafiya ka bi ta da shekara.

Abokin cin mushe ba aboye masa wuka.

Daudar gora a ciki kan shanye ta.


An raba hankali biyu, an ce da Rago ya sha ruwa ya tafi gona

Ba amfanin shiga sharo ba shanu

[AN BAKARA GODIYA DA KWANAN GARKE.

Garin banza a faro-faron banza yake tafiya

Idan wani ya yi rawa an bashi lada, wani in ya yi duka zai sha

In zaka huta, ka huta a babbar innuwa

KADA GARIN GYARAN GIRA A RASA IDO.

KOWA YA BAR GIDA GIDA YA BARSHI

Kowa ya ci ladan kuturu, ya yi masa aski

Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha

Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

Kowa ya daka rawar wani, ya rasa turmin daka tasa

Kowa ya ga gidanka, ka ga nasa

Kowa ya ga na gida, ya kashe ahu

Kowa ya raina gajere, bai taka kunama ba

Kowa ya raina mafari, ba zai yi tabarma ba

Kowa ya sake, a yi masa sakiya

KOWA YA SAMI RANA SAI YAYI SHANYA.

Kowa ya yi zagi a kasuwa, ya san da wanda ya ke.

Tafiya da wuri tafi tafiya da wurwuri

ZAKARAN DA ALLAH YANUFA DA CHARA, ANA MUZURU, ANA SHAHO SAI YA YI.

^
^
Top

<---The End--->

Thats all folks!

^
^
Top

2001 by Dandali.com
Unique Hits since December 2001


.
Sub MenuLinks